Labarai
Babban Layin Lantarki Na Kasan Nan Ya Sake Lalacewa
An sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasar nan a ranar Alhamis.
Layin ya lalace ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda ya jefa miliyoyin ‘yan ƙasar da kuma sana’o’insu cikin duhu.
Wannan ne karo na huɗu da ake samun irin wannan matsalar a shekarar 2024.
Tuni kamfanonin samar da lantarki suka nemi afuwar kwastomominsu tare da sanar da su cewa “waɗanda abin ya shafa suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an shawo kan matsalar”.
Ya zuwa ƙarfe 4:00 na yammacin Alhamis ɗin, kasar ta samar da lantarki mai yawan megawatts 2,984 ne kacal cikin kusan 8,000 da take iya tattarawa.
-
Labarai4 days ago
Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Ilimi6 days ago
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Kwangilar Hanyar Kiyawa Zuwa Birnin Kudu
-
Fasaha6 days ago
Kasuwar Panteka Ta Kaduna Ta Samu Lasisin Koyar Da Sana’o’i —NBTE
-
Labarai6 days ago
Sheikh Bin Uthman Ya Jaddada Muhimmancin Rikon Amana Ga Jami’an Hukumar Alhazai
-
Labarai4 days ago
Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana
-
Labarai6 days ago
Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar
-
Labarai6 days ago
Varane zai bar Manchester United