Labarai
Alhazai Za Su Biya Miliyan Bakwai Don Sauke Farali
Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bukaci maniyyatan aikin Hajjin bana da su biya karin Nera Miliya Daya da Dubu Dari Tara kan kudaden da suka biya a baya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito da yammacin ranar Lahadi mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara.
Fatima Usara ta kara da cewa hukumar ta kuma bada wa’adin ranar 29 ga Maris a matsayin ranar da za a kammala bada cikon kudin.
Ta ce hakan ya zama wajibi duba da yadda darajar Naira ke faduwa a kowacce rana.
A baya dai hukumar ta tsayar da naira miliyan 4 da dubu dari 5 a matsayin kudin aikin Hajjin, kafin daga bisani ta kara naira dubu dari 4, ya zama naira miliyan hudu da dubu 9, sai kuma yanzu da ta sanar da karin kusan naira miliyan biyu.
Idan har wannan kari ya tabbata a yanzu, farashin kujerar aikin hajji zai tashi kan Naira miliyan 6 da dubu dari 9.
A watan Fabarairun da ya gabata ne Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta kayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kudin kuejrar hajjin bana.
Sai dai tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar kara wa maniyyatan kudi bisa dalilan faduwar darajar naira.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
