Labarai
Sojojin Nijeriya Sun Kubutarda Mutane 16 a Kajuru
Sojojin Najeriya ƙarƙashin runduna ta ɗaya sun kuɓutar da mutum 16 da ƴanbindiga suka sace a yankin Kajuru da ke jihar Kaduna.
Sun kuma daƙile yunƙurin wata ƙungiyar miyagu na yin garkuwa da mutane.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, rundunar ta ce sojojin da aka tura ƙarƙashin runduna ta ɗaya sun daƙile yunƙurin sace mutane tare da ceto mutanen da aka sace a yankin Tantatu da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
A cewar sanarwar, sojojin sun kai samamen ne bayan bayanan sirrin da suka samu ranar Lahadi da daddare lokacin da suka bi sawun ƴanbindigar da suka sace wasu mutane a ƙauyen.
“Da isar su wajen da lamarin ya faru, sojoji sun bi ƴanbindigar, inda suka yi musayar wuta daga bisani kuma suka kuɓutar da mutum 16 da aka sace,” in ji sanarwar.
“Sojojin na ci gaba da gudanar da bincike a cikin dazuka domin ganowa tare da tseratar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su tare da murƙushe miyagun ayyukan ƴanbindigar.”S
hugaban hafsan sojojin ƙasa Taoreed Lagbaja ya yaba wa sojojin kan ƙoƙarin nasu tare da neman su ƙara ƙaimi wajen fatattakar masu aikata ta’addanci.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
