Connect with us

Ilimi

Sudan ta Kudu ta Rufe Makarantun Kasar Saboda Tsananin Zafi

Published

on

Gwamnatin Kasar Sudan ta Kudu ta sanar da cewa za ta rufe duka makarantun ƙasar daga ranar Litinin sakamakon tsananin zafin da ake fargabar ƙasar za ta fusakanta.

Ma’aikatun ilimi da na lafiya sun bayar da shawara ga iyayen yara kan yara su zauna a gida sakamakon ana fargabar zafi a ƙasar zai kai har maki 45 a ma’aunin Celsius.

Ma’aikatun sun yi gargaɗi kan cewa duk wata makaranta da aka kama a buɗe za ta fuskanci hukunci wanda hakan zai iya kaiwa ga har a ƙwace lasisinta.

Duk da cewa ma’aikatun ba su sanar da tsawon lokacin da makarantun za su kasance a rufe ba, amma hasashen yanayi ya nuna cewa za a shafe kusan mako biyu ana fuskantar wannan zafin.

Ma’aikatun sun ce za su ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da sanar da jama’a yadda ya kamata.

Peter Garang, wani mazaunin Juba babban birnin kasar, ya yi maraba da matakin.

Ya ce “ya kamata a saka wutar lantarki a makarantu” domin a samu damar shigar da na’urorin sanyaya ɗaki.

Sudan ta Kudu wadda tana daga cikin sabbin ƙasashe a duniya, na fama da matsalar sauyin yanayi tare da tsananin zafi na gama gari amma ba kasafai yake kai maki 40 ba a ma’aunin Celcius.

Rikicin cikin gida dai ya addabi kasar da ke gabashin Afirka wadda ita ma take fama da fari da ambaliyar ruwa, lamarin da ya jefa mazauna kasar cikin wahala.

AP
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai9 hours ago

Ma’aikatan Ceto Na Cigaba Da Neman Jirgin Shugaban Kasar Iran Da Ya Bace

Da yammacin yau lahadi ne tarin ma’aikatan ceto suka bazama wajen aiki gano jirgi mai saukar ungulu dauke da shugaba...

Labarai4 days ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai4 days ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai4 days ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi4 days ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai5 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai5 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai6 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai6 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai6 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Mafi Shahara