Fasaha
Mutane 3 Sun Mutu a Salga a Kano

Mazauna kauyen Yar’Gwanda dake karamar hukumar Tsanyawa ta Kano suna zaman jimami sakamakon rasuwar wani tsoho mai shekaru 60 mai suna Malam Danjuma da dansa Ibrahim mai shekaru 35 da haihuwa da kuma abokinsa Aminu Gaye da suka mutu a salga ko makewayi a kokarin cire wata wayar salula da ta fada a Masai irin na gargajioyar nan.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa daga tashar kashe gobara ta Tsanyawa cewa wasu mutane hudu sun makale a a salga ko masai na gargajiya a lokacin da suke kokarin dauko wayar salular da ta fada.
Ya kuma jaddada cewa, nan take aka tura tawagar ceto zuwa wurin inda aka gano cewa Danjuma ya yi kokarin dauko wayarsa da ta fada cikin bandakin, inda ya makale. Bayan haka, dansa ya shiga bandaki don ya ceci mahaifinsa shi ma shiru sai abokinasa Gaye da Alasan suma sun shiga ne domin ceto mutanen biyu kuma suma suka makale.”
Saminu ya bayyana cewa, an ceto mutanen 3 na farko a sume yayin da na hudun na raye.
Jami’in hulda da jama’a ya ce rundunar ‘yan sandan ta kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin musamman na Bichi inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwar mutane ukun yayin da na hudun mai suna Abba Alhassan mai shekaru 28 a duniya yana samun kulawar likitoci.
Ya ce an mika wadanda suka mutun ne ga baturen ‘yansandan Tsanyawa Iro Lado.
Saminu ya bukaci jama’a da su daina jefa kansu cikin hadari, ya kuma shawarce su da su kai rahoton faruwar gobara, nutsewa, rugujewar gine-gine, da hadurran mota da dai sauransu zuwa ofishin hukumar kashe gobara mafi kusa da su ko kuma ta lambobin wayarsu na dake aiki ba dare ba rana.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
